Gaisuwa daga kamfanin so, harabar kauna, gida mai lambar zuciyata layin
begen ki, zuwa ga rabin rayuwata.
Aduk
lokacin dana tunaki cikin zuciyata nakan ji dadadan kalamanki sunayi min rada
musamman ma ina tuna farkon lokacin da sonki yasamu wurin zama na dindin din
acikin zuciyata, hanya daya danake samun sassauci daga azabban ciwon sonki
dayake addabata shine; in kwanta gami da tunano ki yanayi kallonki, murmushinki
mai sace zuciya hakan kesanyawa naji kamar zaune muke dake muna gunar da
ni'imtacciyar soyayya.
Zuciyarki
ta zama takarda, tawa ta zama biro in rubata miki shafin kauna !